Sports

Masha Allah : Gwarzon Dan Kwallon Nigeria Ahmad Musa Ya Samu Karuwa

Matar babban ɗan wasar tawagar Super Eagles na Najeriya, Ahmed Musa ta haihu kamar yadda fitaccen ɗan wasar ya sanar a dandalin sada zumunta.

Julie ta haifi ɗa namiji, wannan shine haihuwar ta na biyu tare da ɗan kwallon. A baya ta haifa masa ƴa mace.

Ahmed Musa yana da wasu ƴaƴa biyu da tsohuwar matarsa ta haifa masa kafin ya auri Julie.

Da ya ke sanar da labarin, ɗan kwallon ya mika godiyar sa ga Allah da kuma dukkan wadanda suka taimaka masa da iyalinsa da addu’a.

Ya rubuta;

“Rai kyauta ce daga Allah kuma Allah cikin ikonsa ya bamu kyautar da kuɗi ba za ta iya siya ba. Allah ya bawa iyali na ɗa namiji a safiyar yau… Mahaifiyar ɗan da ɗan duk suna cikin ƙoshin lafiya. Mun gode da addu’a ga goyon baya.”

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button