Addini

Hukuncin Kisa Zagin Iyaye Da Annabawa Da waliyyai A Addinin Kiristoci ~ Datti Assalafy

Advertisment

A cikin addinin Kirista ba wai mutum ya zagi Annabi kawai a kashe shi ba, duk wanda ya kuskura ya zagi Babanshi ko Mamanshi Littafiin Injila (Bible) wanda Kiristoci sukayi imani dashi yace a kashe wanda ya zagi Babansa da Mamansa

Ga hujjoji nan daga cikin Littafin Injila:

-A cikin Littafin Matta (Matthew) sura 15 aya 4 Injila (Bible) yace: ku girmama Mahaifinku da Mahaifiyarku, amma duk wanda ya fadi mummunan magana ga Mahaifinshi ko Mahaifiyarshi to a kashe shi

-A cikin Littafin Fitowa (Exodus) sura na 21 aya na 17, Injila yace: duk wanda ya zagi Babanshi ko Mamanshi to dole a kashe shi

-A cikin Littafin Firistoci (Leviticus) aya 20 sura 9 Injila yace: idan akwai wanda ya zagi Mahaifinshi ko Mahaifiyarshi to ya zama dole a kamashi a kashe shi

-A cikin Littafin Karin-Magana (Proverbs) aya 30 sura 27 Injila yace: duk kwayar ido da ya yiwa ubansa mummunan kallo to a cire idon a jefawa ungulu su cinye

-A Littafin Fitiowa (Exodus) sura 21 aya 15, Injila yace: duk wanda ya yiwa Babansa hari ko mahaifiyarsa to a kashe shi

Jama’a wannan fa Bible yake magana akan hukuncin kisa ga wanda ya zagi Babanshi ko Mamanshi, to ina kuwa gawanda ya zagi Annabi wanda ya fi iyaye da waliyai daraja?

A cikin Littafin Firistoci (Leviticus) sura 24 aya 12 zuwa 16 Bible yace duk wanda ya zagi Annabi ko wani waliyyi ko mutum mai tsarki to jama’a su kama wanda yayi zagin su la’anceshi sannan su taru su jefeshi da duwatsu har sai ya mutu

Shi addinin kiristanci da kuke ganinsa dokokin dake cikinsa ma yafi na Musulunci tsanani, akwai ayar da ke cewa duk garin da basu karbi sakon Yesu Almasihu ba to ya zama wajibi a taru aje a yaki mutanen garin a kashe su

Kunga Musulunci yayi sassauci, babu tilas a addini, duk wanda yaga dama ya kafurce anan duniya yayi wa kansa wutar jahannama na jiransa zai tabbata a cikinta har abada, sannan Musulunci yayi sassauci ga wanda ya zagi iyayenshi, ko waliyai da Annabawan Allah, zagin Annabi ne kawai Musulunci yace ayi kisan wanda ya zageshi

Satar amsa gareku Musulmai, duk wanda kuka ga yazo yana kalubalantar hukuncin kisa to ba Musulmi bane mace ne ko na miji kuma kowa wayeshi, kuma ba kirista bane ba musulmi bane, kafuri ne marar addini ya saka rigar addini yake munafurci da takiyya don samun mafaka

Yaa Allah Ka jarrabi masu kalubalantar hukuncin kisa da tabewa da hauka da kaskanci Amin

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button