Kannywood

Wata Sabuwa ! Kalli Bidiyo Wallahi Zan Dauki ƙwaƙwaran Mataki Akan ‘Yan Youtube ~ Teema Makamashi

Advertisment

Jaruma Fatima Isa Muhammad wadda a ka fi sani da Teemah Makamashi ta ko ka kan yadda ‘yan youtube su ke bata suna da sunan neman kudi.
Jarumar ta saki bidiyo ne a shafin ta na Instagram cike da bacin rai inda take fadin yadda wa su ke amfani da sunan ta a shafukan su inda su ke aibatata a duniya kowa ya na kallon ta a matsayin mara mutunci da tarbiya.
Teemah Makamashi ta ce” Sau tari sai a nemi wanii bangare wanda ya fi kama da batanci a saka shi a ciki sai an shiga ciki a ga ba haka bane, da yawa mutane ba sa bibiyar abun da yake cikin abun kawai sai su duba abun da a ka rubutu a saman da a ka rubuta, kuma su zauna a kai, domin haka ina magana da babbar murya daga yau duk wanda ya sake hakan gaskiya bazan yarda ba, sai na bibiye shi duk inda yake wallahi”. A cewar Teemah Makamashi.

Ta ci gaba da cewa“ Ban hana neman kudi da sunana ba, amma bana son a bata min suna, domin abun alfahari ne a ce ka yi silar samun wani, amma duk wanda ya yi yunkurin bata min suna wallahi bazan yarda ba, na farko duk inda ya ke sai na binciko shi. Sannan kuma zan yi bidiyo na musamman na bata duk wata hanyar da mutum zai samu kudin mu ga kuma ya ya zai yi“. Inji Teemah Makamash

Ga bidiyon nan da ta wallafa a shafinta na instagram sai saurara da kunnenku.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button