Tsohon ‘Dan Shekara 70 Ya Aikata Laifin Fyade
Datti Assalafy ya ruwaito Rundinar ‘Yan sandan Nigeria reshen jihar Yobe ta kama wannan tsoho mai suna Yusuf Sa’idu mazaunin unguwar Pompamari garin Damaturu jihar Yobe mai shekaru 70 bisa laifin yiwa wata yarinya karama ‘yar shekara 10 fyade
Kakakin ‘yan sanda na jihar Yobe ASP Dungus Abdulkareem ya gabatar da tsohon wa manema labarai
Yarinyar ta bayyana cewa tsohon ya kirata har gidansa da niyyar zai sayi koyi da take talla, shine sai ya bata Naira 200 sannan ya bata wani abu taci, daga nan ne hankalinta ya gushe ya samu damar da yayi mata fyade
Da ake zantawa da Tsohon ya amince da laifin da ya aikata, inda yace jarabace ta kamashi ba boka bane ya sashi yin lalata da yarinyar, wai sharrin shaidan ne
Yaa Allah Ka tsare al’ummah daga sharrin masu aikata laifin fyade Amin