Labarai

Barrister Abba hikima ya fadi sahihancin hukuncin zaben kaduna

Mutane sun shiga rudani yayinda wasu jaridu su nuna zabe bai kammala ba “inconclusive” wasu jaridu kuma su nuna cewa kotu ta tabbatar da nasarar uba Sani na jam’iyar Apc.

Shine matashin lauyan nan da ke jihar kano a arewacin najeriya barr. Abba hikima ya fadi gaskiya abinda ya faru a kotu da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta kamar haka.

Barrister Abba hikima ya fadi sahihancin hukuncin zaben kaduna
Barrister Abba hikima ya fadi sahihancin hukuncin zaben kaduna

“Babu wata sarkakiya a hukuncin Kaduna. Kotu ta kori karar jam’iyyar PDP saboda abunda tace rashin bin ka’ida wajen tafiyar da shariar.

Amma a irin wadannan shari’un koda kotu ta kori kara akan wasu dalilai na rashin cika ka’idar sharia wajen tafiyar da kara, akwai wajibci akan kotu ta kara gaba ta fadi ra’ayin ta akan ainihin takaddamar dake gabanta. Saboda wannan shi zai bawa kotun sama damar duba hukuncin guda biyu saboda kotun saman ta fadi nata ra’ayin.

Wannan ne yasa kotun tayi gaba tace idan kuma ya zama kotun tayi kuskure a korar karar da tayi, to zata fadi cewa zaben Kaduna bai kammala ba (inconclusive). Wannan ba shi yake nufin za’a sake zaben ba domin an kori karar.

A takaice an kori kara. Idan PDP bata daukaka kara ba, Uba Sani ne zai ci gaba da mulki.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button