Shin Tabbas Hakane ! Sakacin iyaye ya kan jefa ‘ya ‘ya mata hatsarin fyade – Mansura Isah
Tsohuwar jarumar Kannywood, Mansurah Isah ta ce matsalar cin zarafin mata da kananan yara da a yanzu matsalar ta kai kololuwa a matsayin wata matsala da ya kamata a ce kowa ya shigo domin a dama da shi wajen yakar wannan mummunar dabi’a a fadin kasar nan.
Jarumar ta bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin mu dangane da irin rawar da take takawa wajen kawar da wannan matsalar, kasancewar ta shugabar Gidauniyar Today Life Foundation, wadda take tallafawa mata da kananan yara.
Jarumar ta ce”To daman tun kamar shekaru biyu da su ka wuce mun shirya wani gangami na jarumai wanda mu ka hada manyan jarumai da su ka hadar da Sani Danja, Yakubu Muhammad, Muhibbat Abdussalam, Fati Shu’uma da sauran jarumai da dama har da ma daliban jami’a domin yekuwar wayar da kan jama’a dangane da illar fyade da kuma tallace-tallace na yara kanana musamman mata. A wannan lokacin mun yi hoton bidiyo mu ka yada shi, domin fadakarwa yadda mutane za su fadaka kuma su san matakin da za su dauka domin kare kan su, sannan mun jawo hankalin hukuma domin ita ma ta san matakin da za ta dauka domin sauke nauyin da ya kamata na kare lafiya da hakkokin jama’ar kasa. Kuma Alhamdulillahi, mutane sun karbi sakon. To Amma lokacin da yake abun bai zama ya yi karfi sosai ba, sai ya zama mutane ba su mayar da hankali da sakon ba, to yanzu kuma sai ga shi abun ya yi yawa ya zama ruwan dare, kullum idan ka je ofishin Hisba ko na ‘yan sanda za ka ga korafin ya yi yawa, to gaskiya abun ya na tsorata iyaye musamman mu ma su kananan yara, domin yanzu ‘ya ta ko bakin kofar gida ta fita da sauran kannen ta maza hankali na ba ya kwanciya, to yanzu wannan abubuwan da su ke faruwa ya sa mu iyaye kullum cikin tsoro da fargaba mu ke. Ka duba cewar yarinya ‘yar wata uku a ka je a ka dauke ta a gaban mahaifiyar ta a ka keta mata haddi, to irin wannan abun sai dai addu’a, sannan kuma iyaye su rinka kula tare da saka idanu a kan ‘ya ‘yan su”.
Ta ci gaba da cewa “Kuma gaskiya akwai iyayen da su ke sakaci da yaran su, musamman ma mu a nan Arewa, kuma musamman tsohuwar al’adar kunyar dan fari, yadda zai zamo ba za ka yi mata fada ba, ba za ka kalle ta ba. To irin wannan ya kan jefa yara cikin wata rayuwa. Kuma idan ta samu kanta a wannan halin fa, babu mai auren ta sai dai a kai ta wani gari daban, domin idan a garin da a ka san ta ne, duk wanda ya fito neman ta za a ce da shi ai ga abun da ya faru da ita tun ta na karama. Kai za ma a rinka kiran gidan su da abun da ta aikata ne. Saboda haka dole ne mu fito mu bada lokacin mu, domin yakar irin mutanen nan da su ke bata kananan yara. Kuma babbar masifar da a ka fi fuskanta shi ne, wani lokacin ma abubuwan daga gida a ke yin su. Saboda mun sha gani Uba ya yi wa ‘yar da ya haifa, ina da wannan matsalar a gaba na, kuma yarinyar ta na tare da ni a yanzu, duk da a wajen kakar ta take, amma duk abun da ya taso na kulawar ta, ni ce na ke yi a karkashin Gidauniyar Today Life Foundation, kuma daga zuwa karbar kudin abinci a wajen mahaifin ta kawai sai ya ce sai ya neme ta in ba haka ba ba zai ba ta kudin ba, da haka ya lalata ta yanzu ya gudu ya koma Legas. Kuma ‘yan uwa dangin uwa ko dangin mahaifin su ma na bada gudunmawa a cikin harkar, to dole iyaye su kara kula duk wani kannen ki ko kuma kannen mijin ki da zai rinka daukar yaran ki ya na dora su a kan cinya, ki ce ba ki yarda ba ki hana shi kwata-kwata”.
To sai dai kafin mu karkare hirar ta mu da Mansurah Isah, ta ja hankali ga iyaye cewa da su kara kula da amanar da Allah ya dora mu su ta tarbiyyar ‘ya’ yan su, domin kuwa aiki ne babba da ya kamata su tsaya a kan ‘ya ‘yan su tare da neman taimakon Allah wajen yin addu’a.