Majalisar koli ta JIBWIS ta ziyarci Bafarawa domin godiyan kyautar makekiyar makaranta ( A cikin Hotuna)
Daga Ibrahim Baba Suleiman
Majlisar koli ta kungiyar JIBWIS, tare da wasu wakilan kwamitoci a matakin kasa da wasu takaitattun shugabannin jihohi sun ziyarci Tsohon gwamnan jihar Sokoto Dakta Attahiru Dalhatu Bafarawa, domin yi masa godiya akan kyautar makekiyar makaranta wanda ya kashe mata sama da miliyan dubu daya da dari biyar a shinkafin Jihar Zamfara.
Shugaban JIBWIS Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau shi ya jagoranci tawagar tare da manyan malaman kungiyar. “Mun niko gari takanas ta kano domin muzo da dukkan mutanen mu dake fadin Naijeriya, mu nuna farin cikin mu na kyautar wannan makaranta da ka yiwa wannan kungiya mai albarka, kuma bamu da wani Abu da zamu maka illa muyi ta maka addu’a Allah ya saka maka da gidan aljanna” inji Sheikh Bala Lau.
A lokacin da yake mai da bayani, Tsohon gwamna Attahiru Bafarawa, yace yayi wannan aiki ne da kyakkawar niyya, tare da fatar Allah ya amshi wannan aiki. “Kungiyar Izala kungiyar mu ce ta addini, kuma muna kallon ayyukan da shugabanni sukeyi, domin ganin addinin Allah yaci gaba, muna kuma kyautata zato na alheri ga wadannan shugabanni, Dan haka muna nan zamu ci gaba da yin abun da zamu iya daidai gwargwado har zuwa lokacin da zamu koma ga mahaliccin mu. Kazalika muna fatar addu’oin da kuke mana Allah ya karba.