Labarai

Masarautar Shinkafi Taci Amanar Musulmi Kuma Taci Amanar Arewa ~ Datti Assalafy

Advertisment

Yau na wayi gari da wani mummunan labari na cin amanar Musulunci kuma cin amanar Arewa da zubar da daraja da mutuncin manyan Sarakunan Musulunci masu tutiya da jihadin Shehu Usman Dan Fodio wanda Masarautar Shinkafi tayi

Jiya Litinin Mai Martaba Sarkin Gabas na Shinkafi Alhaji Muhammad Isa Makwashe  ya kira bakin bamaguje mai bayyana tsananin kiyayyarsa ga Musulunci da Musulmai da kuma Arewa mai bayyana tsananin batancinsa ga jihadin Shehu Usman Dan Fodio wato Femi Fani Kayode  (FFK) inda ya nadashi Sarautar “Sadaukin Shinkafi” na jihar Zamfara

Hakika wannan abu da ya faru shine mafi munin cin mutuncin Sarautar Gargaji na Arewa da aka yi tun bayan cin mutuncin da turawan mulkin mallaka da ‘yan Demokaradiyyah suka yiwa Manyan Sarakunan Gargajiya, sannan anci mutuncin addinin Allah, domin sarautun suna tutiya da Musulunci ne.

Wanda bai fahimci waye Femi Fani Kayode ba da kuma mugun nufi da yake dashi a kan Musulunci ba to ga bayani a takaice, FFK bayarbe ne, tsohon Minista sufurin jiragen sama, babban jigo a siyasar Goodluck Jonathan, a shekarar 2016 Femi Fani Kayode ya wallafa rubutu a shafinsa na Facebook inda yayi kira ga sabon shugaban Kasar Amurka Donald Trump da ya zo Nigeria ya rusa Musulunci da Musulmai

Femi Fani Kayode yace duk wani Musulmi ‘dan ta’adda ne, babu abinda Musulunci yake koyarwa sai ta’addanci, yace Musulmai ne suka hana Nigeria da duniya zaman lafiya, yace an kafa Musulunci ta hanyar ta’addanci, yace ‘yan Arewa musamman Hausa Fulani annoba ne, kuma bakin haure ne da suka zo daga Kasashen Guinea Bissau, Sudan, Mali da Chadi, bai taba daukar mu a matsayin ‘yan Arewa ba saboda Musulunci da muke bi, amma baya yin batanci ta bangaren da mabiya addinin nasara ke da yawa

Ya zagi Shehu Usman Dan Fodio, yaci mutuncinsa ya bata da’awarsa, ya kirashi a matsayin kakan ‘yan Boko Haram da sauran kungiyoyin ta’addanci, to wannan mutumi aka dauko aka bashi sarautar Sadaukin Shinkafi saboda tsabagen cin amanar Musulunci, ya gama bata Musulunci a idon duniya yau Kasar Arewa inda ake tutiya da Musulunci an daukoshi an karramashi da Sarauta

Muna kira da a gaggauta tube rawanin Sarautar Sarkin Gabas din Shinkafi sannan a kwace sarautar da ya bawa Femi Fani Kayode, muna kira ga majalisar koli na addinin  Musulunci karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Saad Abubakar III da Sauran manyan Sarakunan yanka na Musulunci da su dauki mataki a kan wannan cin amana da aka yi, wallahi anci zarafin mu, anci zarafin Musulmai da Arewa

Duk wani Musulmi da zai zauna inuwa daya da Femi Fani Kayode to ba mutumin kirki bane, balle har ya jawoshi jikinsa ya bashi Sarautar Musulunci, cin amanar Musulunci ne, muna kira ga jama’ar Zamfara musamman shinkafi da su bijirewa umarnin Sarkin Gabas din Shinkafi, a masa tawaye

Duk wanda yake da hannu a wannan cin amana da akayi Allah Ka isar mana, Allah Ka nuna masa aya, Allah Ka wulakantashi kowaye

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button