Labarai

Sallah: Tsohon Gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari ya raba shanu 400

A yau Laraba ne tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ya fara rabon shanu 400 ga magoya bayansa da ke kananan hukumomi 14 da na mazabu 147 na jihar.

An raba shanun ne domin al’ummar jihar ta Zamfara su gudanar da bukukuwan Ƙaramar Sallah cikin nishadi.

Shugaban magoya bayan Yari, Alhaji Lawal M Liman Gabden Kauran Namoda ne ya mika shanun ga wadanda suka amfana a Gusau Babban birnin Jihar.

Ya lissafa wadanda su ka ci gajiyar tallafin waɗanda su ka hada da malaman addinin musulunci da kungiyoyin matasa da mata da tsofaffi da kuma shugabannin al’umma a jihar.

“Kananan hukumomi goma daga cikin 14 na jihar sun riga sun karbi shanu da aka ware musu,” inji Liman.

Gabden Kauran Namoda ya yabawa tsohon gwamnan bisa yadda ya ke nuna damuwarsa ga al’ummar jihar musamman wadanda su ke masu karamin karfi.

Daily Nigerian hausa na ruwaito Liman ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi amfani da Wannan lokaci na watan Ramadan domin yin addu’o’in samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar da ma Najeriya baki daya.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button