Labarai

Da Dumi Dumi : Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Zai Tafi Mali

Shugaban Najeriya Miuhammadu Buhari zai tafi Bamako babban birnin ƙasar Mali a ranar Alhamis.

Tafiyar ta shugaban ƙasar ta biyo bayan tattaunawarsa da Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, wanda yana daga cikin masu shiga tsakani daga ƙunigyar ECOWAS da suka je Mali domin kawo sasanci.
Wasu daga cikin shugabannin ƙasashen Yammacin Afrika irin su Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou sun amince su hadu a Mali domin tattaunawa domin kawo sasanci tsakanin Shugaban Mali Boubacar Keita da kuma ‘yan adawa a ƙasar.
Ana sa ran Shugaban Ghana Nana Akufo Addo da kuma na Cote d’Ivoire Alassane Ouattara za su halarci tattaunawar.bbchausa na ruwaito.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button