Labarai

Aisha Buhari ta wallafa bidiyon Sanatocin da suka soki gwamnatin tarayya

Advertisment

Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha ta wallafa bidiyon sanatoci biyu dake sukar gwamnatin tarayya a shafinta na Twitter @aishambuhari a ranar Juma’a, 19 ga watan Janairu.

A ranar Laraba, Sanata Isah Misau dake wakiltan Bauchi ta tsakiya a majalisar dokokin jihar ya caccaki nadin darakta janar na hukumar liken asiri da akayi inda ya nei sanin ko ya cancanci hawa wannan mataki.

Har ila yau Aisha Buhari ta sake wallafa wani bidiyo na sanata mai wakiltan Bayelsa na gabas, Ben Murray-Bruce, inda yake sukar gwamnatin tarayya tare da ikirarin cewa Najeriya ta kasance kasa mara doka.

Wannan sune abu na farko da uwargidan shugaban kasar ta wallafa a shafinta Twitter tun bayan gaisuwan bikin Kirsimati da tayi a ranar 25 ga watan Disamban 2017.

Advertisment

Sources :Naij com

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button