Subhanallahi ! Ya Yiwa ‘ Yar Cikinsa Fyade Tana Dauke Da cikin Wata Hudu
Rundinar ‘yan sandan Nigeria sun cafke wannan mutumi mai suna Umaru Maigoro ‘dan shekara 53 wanda ya yiwa ‘yar cikinsa da ya haifa fyade ‘yar shekara 14
A sanadiyyar fyade da ya yiwa ‘yar sa, ciki ya shiga wata hudu, yarinyar tana makarantar sakandare aji uku, mutumin mazaunin unguwar Pampomari ne dake layin Damakasu cikin garin Damaturu jihar Yobe
Bayan ya yiwa ‘yar tasa fyade daga bisani ta fada masa ciki ya shiga, shine sai ya dauketa ya kaita kauye domin ya boye mummunan ta’asar da ya aikata, anan ne asirinsa ya tonu, da ‘yan sanda suke tuhumarsa ya amince da laifin da ya aikata, inda yace ya sha yimata fyade, bai iya kirga adadin fyade da ya mata kafin ciki ya shiga
Mutumin sananne ne yana sana’ar sayar da goro a babbar tashar mota na garin Damaturu, ya fara yiwa ‘yar cikinsa fyade bayan ya saki mahaifiyar yarinyar, daga bisani ya auri wata mata, idan ‘yan sanda sun kammala bincike zasu gurfanar dashi a kotu domin ya girbi sakamakon abinda ya aikata na abin kunya da zalunci
Yaa Allah Ka kare jama’ar Musulmi daga sharrin masu fyade da kuma bokaye Amin
Daga Datti Assalafiy