Labarai

Jarumta ko Tsoro : “Bana tsoron mutuwa amma ina son sulhu” – Bello Turji

Advertisment

Bello Turji ya kuma nemi gwamnatin Zamfara ta sanya shi cikin kokarinta na samar da zaman lafiya a jihar.

Turji ya sanar da haka ne a wani bidiyo da ya yi bayan sojoji sun kashe Halilu Sububu.

A baya-bayan nan jami’an tsaro sun hallaka manyan jagororin ’yan
bindiga a Zamfara.

Haka ta faru ne musamman bayan tsohon gwamna jihar kuma Karamin Ministan Tsaro, Muhammad Bello Matawalle da manyan kwamandojin soji sun tare a can da nufin ganin bayan ayyukan ’yan fashin daji.

A jihohin Kaduna da Katsina da Neja ma wasu gawurtattun ’yan bindiga sun gamu da ƙarar kwana a lokuta daban-daban a baya-bayan nan.

A cikin bidiyon Turji na ta’aziyyar Halilu Sububu, an ji shi yana cewa
ragargazar da sojoji suka yi ba za ta sa su saduda ba.

Amma sai ya ƙara da neman afuwa da sulhu inda ya nemi gwamnatin ta zo su zauna su tattauna a fahimci juna, wanda a cewarsa, hakan zai samar da zaman lafiya a Zamfara da ma ƙasa baki ɗaya.

A ’yan baya-bayan nan sojojin Najeriya na ci gaba da samun nasara a yaƙinsu da ’yan bindigar da yaƙi ci yaƙi cinyewa shekara da shekaru.

Kazalika rikici tsakanin ƙungiyoyin ’yan fashin daji ya yi sanadiyyar
mutuwar wasu manya daga cikinsu tare da yaransu.

Ga mai son download din wannan video ga link nan.

DOWNLOAD VIDEO HER

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button