Kasar Ingila Ta Yi Allah Wadai Da Hukuncin Kisa Kan Wanda Ya Yiwa Annabi (SAW) Batanci A Kano
Kasar Ingila a karin farko ta yi magana akan hukuncin kisan da aka yankewa Yahaya Umar Sharifai na kisa bayan samunsa da laifin yiwa annbi kalaman batanci.
Tace ta yi Allah wadai da hukuncin sannan kuma tana nan tana bibiyar yanda lamura ke gudana akan yanke hukuncin. Wanda kunji Yadda kafoffin labarai sunka ruwaito Yanda aka yankewa Yahaya hukunci a kotun shari’ar Musulunci dake Hausawa, Kano.
Kasar ta bayyana cewa, ya kamata a bar kowa ya rika bayyana ra’ayinsa kan duk wani lamari ba tare da takura ba. Sannan tace tana inkari kowane hukuncin kisa.
Ta bayyana bakane a martanin tambayar da jaridar Punch ta aikewa ofishin jakadancin ta na Najeriya inda me kula da yada labaran ofishin jakadancin, Christopher Ogunmodede ya bayyana haka.