Uncategorized

Wata sabuwa ! Tsohon Saurayin Yarinyar Da Shugaban kwastan Ya Aura Ya Makata A kotu Ta Biya shi kudi Sama Da Miliyan Tara ( Hotuna)

Advertisment

TIRKASHI: Tsohon manemin yarinyar da ta Auri shugaban hukumar Custom ya shigar da ita kara yana neman ta biya shi sama da Naira Miliyan tara da ya kashe akan ta tsawon lokacin da suke tare.

Yace yayi hakanne bayan ta wulakanta shi a bainar jama’ah, Kuma ta nemi da ya rubuta duk abunda ya kashe a nemanta za ta biya shi.

Na Biya Mata Kudin Zuwa Kasashen Dubai, Saudiyya, Ingila Da Chana, Don Haka A Biya Ni Dukkan Kudaden Da Na Kashe Mata, Cewar Tsohon Saurayin Amaryar Shugaban Kwastan, Hameed Ali

Daga Ismai’l Karatu

Tsohon Saurayin Hajiya Zainab Abdullahi Yahaya, Amaryar shugaban hukumar Kwastan Hameed Ali ya nemi da ta dawo masa dukkan kudaden da ya kashe mata a lokacin da suke soyayya da suka hada da na tafiye-fiyen da ya biya mata zuwa Saudiyya, Dubai, UK da China.

Saurayin mai suna Zubairu Ɗalhatu Malami, ya bayyana cewa Zainab ta yaudareshi domin ta bayyana cewa babu wanda za ta aura in ba shi ba daga baya ta tsallake shi zuwa wani tsoho mai maiƙo.

Wani babban ɗan jarida mai zaman kansa George Omonya Daniel ya ruwaito cewa babu tabbacin ko Hameed Ali ya san da wannan batu, amma lallai tsohon saurayin ya ce ba zai bari hau ta haushi domin ba zai yi biyu babu ba.

Alhaji Zubairu ya nemi haƙinsa ne ta hanyar lauyansa, inda aka aika wa da tsohuwar budurwar da takarda bukatar biyan waɗannan kuɗaɗe.

A cikin takardar wadda ta bayyana a kafafen sadarwa, Zubairu Dalhatu Malami ya bukaci  ta biyashi jimillan kuɗi naira miliyan tara da dubu tamanin da ɗaya (N9,81,207,45m) tare da dawo masa da katin shaidar aiki a kamfaninsa da ya bata tare da kannenta.

Harwayau ya nemi ta dawo da wasu kayan sawa, kayan aikin kamfanin da kuma kwamfutocin kamfani dake hanunta da kannenta tare da maido da lambar mota mai dauke da sunan karamar hukumar Bichi dake gunta.

Lauyan ya yi barazanar cewa ƙin biyan kudaden tare da dawo da dukkan abinda aka bikata zai iya kaiwa ga daukar mataki a dokace bisa umarnin Alhaji Zubairu Malami.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button