Uncategorized
FATAWAR RABON GADO (79)|DR JAMILU YUSUF ZAREWA
FATAWAR RABON GADO (79)
Tambaya?
Assalamu alaykum, malam mutum ne ya rasu ya bar Mata 1, da diya Mace 1, sai kanne 6. ubansu 1, sai wasu kanne 7. Uwarsu 1, ya za’a raba gadon sa?
Amsa:
Wa alaikum assalam, za’a raba abin da ya bari gida: 8, a bawa matarsa kashi daya, ‘yarsa kashi hudu, Ragowar kashi ukun sai a bawa ‘yan’uwansa da suka hada uba daya.
Allah ne mafi sani
22/11/2016
Dr. Jamilu Zarewa
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com