Uncategorized

Talakawa Ne Ke Haddasa Matsaloli A Kasar Nan, Cewar Solomon Dalung

Talakawa Ne Ke Haddasa Matsaloli A Kasar Nan, Cewar Solomon Dalung 

Barista Solomon Dalung, wanda shine ministan matasa da wasanni, ya ce ko shakka babu talakawa sune matsalar Nigeria. Yace duk sanda kaji wata matsala ko tashin hankali ya kunno kai, to za ka samu talaka ne ya kirkiro ta. Saboda talaka shine bai yadda da dan uwansa ba, bai yadda da addinin wani ba sannan ga bakin ciki da hassada ga junansu. 

Barista Dalung ya bayyana haka ne a wajen taron cin abincin dare na shekara-shekara da hukumar UFUK Dialogue Foundation ta shirya a Abuja.

Masu karatu ko kun amince da kalaman ministan?

©Rariya

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA