Tun Da An Bude Gidajen kallon kwallo a Bude makarantun Islamiyya -Dr Abdallah Gadon Kaya
A cewar Limamin masallacin juma’a na Usman Bin Affan dake unguwar Gadan Kaya Dr Abdallah Usman Umar, gwamnatin Kano ta bude makarantun Islamiyyu domin yara su koma makarantu wajen ganin sun kara ninka addu’o i na rabuwa da cutar Coronavirus.
Dr Abdallah Gadan Kaya a zantawar sa da Dala FM ta cikin shirin Rayuwa Abar Koyi wanda ya gabatar yau Juma’a.
Ya ce” Bude makarantun Islamiyyar zai taimaka matuka musamman ma wajen kara rubanya addu’ar da a ke na Allah S.w.t ya kawar da cuta mai sarkewar numfashi, tun da gwamnatin Kano ta bude gidajen kallon kwallo a Kano, babu shakka kamata ya yi suma makarantun Islamiyya a basu dama su bude domin ci gaba da karatun su”. A cewar Dr Abdallah.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara kaimi wajen dakile yawaitar kashe-kashen al’umma da ‘yan bindiga su ke yi a Arewacin Nijeriya.
Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, Dr Abdallah Usman Umar, ya kuma shawarci ‘yan Jarida da sauran al’umma su guji yada labaran karya domin gudun afkuwar matsala a tsakanin mutane.

![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)





