Labarai

Wani matashi Dan Sahu ‘keke napep’ ya Maida kudi Miliyan 15 da ya tsinta

Wani matashi dake tuka Babur din Adaidaita Sahun mai suna Auwalu Salisu Wanda aka fi Sani da Na Baba dake bayan tashar Yan Kaba, ya dawo da wasu kudi Mallakin Alhaji Ibrahim Barka Daga kasar Chadi da aka manta a babur dinsa ranar Alhamis din data gabata.

Kudin akwai Saifa Milyan 10 da Dubu 130 sai kuma sama da Naira Milyan 2 biyo bayan jin sanarwar cigiyar kudin a tashar Arewa Radio 93.1.

Daga karshe an bashi tukuichin tsintuwa har Naira Dubu ‘Dari 400.

Wani matashi Dan Sahu 'kake napep' ya Maida kudi Miliyan 15 da ya tsinta
Dan sahu mai Fecin kaf mai kuɗi da Kaftani

Ga kalaman yaron da ya tsinci kuɗi :

A ranar alhamis 11:30pm na safe na dauke su daga badawa na aje su kafin aje bata, basan sun manta kayan nasu ba naje yan kaba na sauko zanyi dosta sai naga jaka a bayan mashin dina na dauko na taɓa naji laushi koda na bude sai naga kudi ne a ciki.

Ina zuwa gida na gayawa mamata tace abari baba na yazo bayan ya dawo gida sai nayi masa bayyani yace bari aje wuri domin a sake dubuwa ko zamu ga mutanen muna koma bamu gansu ba domin wajen babba wuri ne.

Sai mahaifina yace azo a aje kuɗin mu saurara muji, bayan nazo sai naji sanarwa a gidan rediyo na arewa Radio sai na dauki number na kira, na kira wayar sau biyar ba’a dauka ba.

Dan sahu ya cigaba da cewa naji dadi sosai da na hadu da mai kuɗin domin na bashi abinsa.” inji Dan sahu.

Ga bidiyon da ankayi hirar nan.

Dan uwan wanda yake da wannan kuɗi yayi magana saboda mai kudin bayajin hausa ga abinda dan uwan ke cewa:

“Duba da irin yanayin da ake ciki tabbas wannan yaro ya samu tarbiyya mai kyau saboda a yadda mahaifinsa yayi mana bayyani cewa jiya ma garin kwaki sun ka chi saboda halin tsada rayuwa da ake ciki.- inji dan uwan mai kudi.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button