Labarai
Sheik Bala Lau Ya Dauki Nauyin Duba Lafiyar Mahaifin Marigayi Sheik Albaniy Zaria
Wannan Dattijo da ake gani a hoto shine mahaifin Malam Albaniy Zaria, har yanzu yana raye, ya kai shekaru 100 a duniya, saboda tsufa da rashin lafiya yanzu ba ya iya fita masallaci.
Shugaban kungiyar IZALA na duniya Sheikh Dr Abdullahi Bala Lau ya turo an duba mahaifin Malam Albaniy, kuma ya sa aka dauke shi aka kai shi asibiti.
Hakika Malam Abdullahi Bala bai ci amanar aminantaka da malunta ba, ka burge mu Malam, mun ji dadin wannan karamci da ka yi mana, Allah Ya biya ka da gidan Aljanna.
Yaa Allah Ka karawa Mahaifin Malam Albaniy Zaria lafiya, Ka ba shi ikon dacewa da kyakkyawan karshe. Amin.
Daga Datti Assalafiy
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com