Uncategorized

Ko Kun San Wa Mc Tagwaye Mai Kama Da Buhari Ya Aura ?

Advertisment

Shahararren mai wasan barkwancin nan da ya shahara wajen kwaikwayon murya da zantuttukan shugaba Muhammadu Buhari mai suna Obinna Simon wanda a ka fi sani da MC Tagwaye ya auri ‘yar mai baiwa Shugaban Kasar Nijeriya shawara a kan kyautata rayuwar Jama’a wato Maryam Uwais.

Kamar yadda BBC Hausa ta wallafa, MC Tagwaye wanda dan asalin kabilar Igbo ne a Jihar Anambra a Kudancin Nijeriya. Kuma ya yi rayuwar sa ne a Jihar Katsina tare da shakikin sa da su ke Hassan da Usaini.

Ko da ya ke MC Tagwaye ya shahara matuka a masana’antar fina-finai da wakoki da ke Arewaci da kuma Kudancin Kasar nan, amma auren na sa ya kasance a cikin sirri ba tare da ya bayyanawa duniya shirin yin hakan ba.

Ango Obinna dai ya yi wuf ne da Hauwa, diyar Maryam Uwais, inda ya wallafa hotunan auren na su a shafin sa na Instagram ya na bayyana murnar sa na wannan aure, da kuma fatan ci gaba da rayuwa kamar yadda a ka saba.

Ita ma sirikar ta sa Maryam Uwais wadda lauya ce sama da shekaru 36, kuma fitacciya ce a kasar nan a kan aikin lauya da aikin kwato hakkin dan Adam da kuma aikin sa kai, ta wallafa auren diyar ta ne da angon ta MC Tagwaye a shafin ta na Instagram, ta na nuna cewa ‘yar ta ta yi aure, kuma ta sami fyallelan siriki.

Maryam Uwais dai ta yi aiki a ma’aikatar shari’a ta jihar Kano da babban bankin Nijeriya da kuma hukumar tantance dokokin Nijeriya (NLRC). Kuma ita ce ta kafa Gidauniyar Isa Wali tun a shekarar 2009 domin taimakawa ilimi da lafiyar mata da kananan yara.

Za mu kawo muku rahoto na musamman a kan cece kuce da mutane ke yi a kan wannan aure da Obinna da Hauwa.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button