Budurcin ‘Ya Mace, Ma’anarsa Da Rabe-Rabensa
ALLAH cikin ikon sa da tsari na halitta irin nasa yasa ana haihuwar kowace mace da budurci, wannan budurcin shi ake kira da “HYMEN” a turance. Ita dai Hymen wata fata ce mai dauke da jini a cikinta, tana cikin farjin kowace mace amma ba tada wuyar fashewa.
Sannan ba wai Hymen kadai ba ce fatar da ke a cikin farjin mace, a’a. Akwai fata biyu wadanda ake kira a turance da “Labia Minora da Labia Majora”, wadannan sune ainahin fatun da ke dauke da farjin mace, amma shi ainahin budurcin yana daga ciki, ma’ana, su wadannan “Labia Minora da Labia Majora” sune suke kare budurcin da ke cikin farjin, kuma wannan fatar ba mai kwari ba ce sosai, sannan tana yagewa dazarar ta samu takura.
MA’ANAR BUDURCI:
Kalmar budurci ta samo asalinta ne daga kalmar budurwa, kuma kalmar tana da harshen damo. Budurwa kuwa a Hausance ita ce ‘ya mace wadda ba ta taba yin aure ba, kuma ba ta taba saduwa da namiji ba. A littafin Risala cewa aka yi “Budurwa ita ce ‘ya macen da cinta, shanta, suturarta, tarbiyarta da hakkin aurar da ita, suka rataya a kan ubanta.
Kenan, ana iya cewa, budurci wani lokaci ne da ‘ya mace ke shiga na tsakanin balagarta zuwa lokacin da ta yi auren farko. Wasu malamai sun kara haske da cewa “Lokacin budurci yakan fara daga shekara goma zuwa sha biyar (15)”.
A wannan lokaci ne za a ga masoya (maza) sun fara kai mata hari da sunan suna son ta. Haka kuma za ta zama abokiyar son kowa; wasannin da ta ke yi da can lokacin kuruciya za ta rage, saboda balaga ta fara shigo ta, ta fara jin kunya; saboda wasu abubuwa sun fara bayyana a jikinta, kamar Nono da sauransu. Kuma a wannan lokaci ne take ji da kanta, tana ganin kanta daidai da kowa.
Idan aka zurfafa cikin ma’anar kalmar budurci, sai a ga ta dauki wani salo na daban. Saboda a ganin wasu masana “Budurci dai shi ne likin da ake debewa lokacin da aka aurar da budurwa; aka sadu da ita. Amma irin budurwar da ke iskanci tun kafin ta yi auren farko, to, ba za a same ta da wannan likin ba, don haka, hausawa na kiran irin wadannan budaren da Sarewa, ko Muna-horo.
Kishiyar kalmar budurwa, ita ce “Zawara”, wanda ke nuna sabanin budurci. Wato lokaci ne tsakanin auren mace har zuwa karshen rayuwarta, ko tana gidan miji ko tana gidan iyayenta matukar ta yi auren farko, to, ta zama zawara.
BUDURCIN ‘YA MACE KASHI BIYU NE:
1. Budurci tsararre
2. Budurcin da ba tsararre ba
Ø Budurci Tsararre: – Budurci tsararre shi ne wanda ba wani abu da ya same shi, yana nan a tsare kamar yadda yake, har sai lokacin da mijinta ya sadu da ita, sannan ya gushe.
Ø Budurcin Da Ba Tsararre Ba: – Budurcin da ba tsararre ba shi ne, budurcin da ya samu matsala sanadiyar wasu dalilai har ya gusar da mutuncin yarinya, ta hanyar saduwa da namiji tun kamin tayi aure, ko kuma ta hanyar da bata sani ba. Shi kuma hakan na iya faruwa ta hanyar tsallake-tsallake, da gudane-gudane, da daukar kaya masu nauyi kamar yadda za mu ji.
Duk Daga Alummata.com