Yan Maiduguri sun yi watsi da yan ta’adda sun koma ga harkar nishadi
Yayin da sojoji ke neman kawo karshen wannan kungiyar yan ta’adda daga ƙasar, matasan Maiduguri inda kungiyar ta samu asali sun koma ga waka domin samun annashuwa daga barnar da yan ta’addar suka yi a garin
Maiduguri babban birnin jihar Borno dake yankin Arewa maso gabashin Nijeriya ta soma komawa kamar yadda take wajen samun nishadi domin matasan garin sun koma ga harkar waka kuma wuraren nishadi sun fara koma yadda suke a da.
Yayin da wasu ke ganin cewa jihar Borno ya koma tamkar kamar filin yaki tsakani yan boko haram da sojoji, wasu matasan jihar suna son su sauya tunanin mu inda suke nuna halin walakin goro a miya game da harkar zamantakewa da nishadi dake faruwa a jihar.
Boko haram ta fara ta’addancin ta a wannan jihar kuma sunyi sanadiyar rasuwar sama da mutane 20,000 tare asarar dukiyoyi fiye da kimani har ma da sa wasu da dama yin balaguro zuwa wata jiha har ma da ƙasashen waje.
Ganin cewa sojin sun fara samun nasara wajen korar wannan kasurgumin ƙungiyar ta’addanci da ta addabi al’ummar jihar matasan garin sun koma ga waka domin nishadantar da junansu don kawar da matsaloli da yan ta’adda suka haifar a zukatan al’ummar jihar.
Sannu bata hana kaiwa da haka matasa suka daura domin faranta ma kansu rai inda suka koma ga nishaɗi domin kawar da barnar da rikicin boko haram ya haifar a jihar su.
Marubucin jaridar Guardian Eromo Egbejule ya ruwaito cewa gidajen shakatawa na dare watau ‘club’ sun cigaba da tafiyar da alamuran su a cikin garin ba tare da fargaba.
Cikin ayyukan da matasan keyi yanzu akwai hada fagen yin wakar domin fitar da basirar su ga idon jama’a.
Mazaunan garin sun samun annashuwa bayan tserewar kungiyar domin neman tsira. Yanzu ƙungiyar kwallon kafa ta jihar watau El-kenemi warriors sun koma da taka-leda a jihar kuma daliban jami’ar Maiduguri sun koma sahun da suka kafa na shirya wasanni don moriyar junansu.
A kwanan baya daliban makarantar sun shirya bikin kammala karatu wadda har ma suka gayyato fitattun mawakan yankin arewa Classiq da Morell