HUKUNCIN BOYE KAYA HAR SAI SUN YI TSADA| DR JAMILU YUSUF ZAREWA
HUKUNCIN BOYE KAYA HAR SAI SUN YI TSADA
Tambaya :
Assalamu alaikum. wata tambaya nake da ita Dr. Wai shin meye gasiyar hukuncin wanda ya sayi kaya a lokacin da suke araha ya boye da niyyar in sunyi tsada ya fito da su ya sayar dan ya sami riba mai yawa? Allah shi dada budi amin
Amsa :
To dan’uwa ya zo a hadisi cewa : “Ba wanda yake boye kaya sai mai zunubi” Tirmizi ya rawaito shi a : 3567, kuma ya kyautata shi, saidai malamai sun yi sabani akan irin kayan da ya haramta a boye da wadanda ba su haramta ba :
1. Akwai wadanda suka tafi cewa : duk wani abu da mutane suke bukatarsa to bai halatta mutum ya siya ya ajjiye ba, da nufin sai yayi tsada ya fito da shi, don haka har tufafi da magunguna bai halatta a boye su ba, saidai idan ya siya ne da nufin ya yi amfani da su nan gaba.
Ko kuma iyalansa, Wannan shi ne maganar Abu-Yusuf babban almajirin Abu-hanifa, kamar yadda yazo a littafin : Daurul-kiyam wal’aklak fil-islam shafi na : 295. Sannan ita ce maganar Malik a Mudawwanah kamar yadda ya zo a : 4291.
2. Akwai malaman da suka tafi cewa ya halatta a boye abin da yake ba abinci ba ne da mutane za su ci su rayu, kamar barkono, zabibi, mai, da sauransu, saboda yawanci mutane suna cutuwa ne idan aka boye abinci. An rawaito wannan daga Abdullahi dan Mubarak da Sa’id dan Musayyib kamar yadda Tirmizi ya ambata a Sunan dinsa 3567 sannan ita ce maganar Shafi’iyya da Hanbaliyya , kamar yadda ya zo a
Raudatu Addalibiina 3411 da kuma Almugni 4154
Wasu malaman suna rinjayar da maganar farko, amma idan ba siyan abin ya yi ba, ya mallake shi ne ta wata hanya, ko kuma ya noma sai ya boye har ya yi tsada sannan ya siyar, to wannan bai haramta ba, ko da kuwa abinci ne, har wasu malaman ma sun hakaito ijma’in malamai akan halaccin haka, kamar yadda ya zo a Jami’ussagir shafi na : 481
Allah ne mafi sani
Amsawa
Dr jamilu zarewa