Labarai
Sojojin Rasha sun doshi birnin Kyiv, fadar gwamnatin Ukraine
Advertisment
Sojoji sun yi ta tona ramuka tare da toshe hanyoyi ta amfani da tankokin yaki na ruwaito
Hukumomin ƙasar sun ce ana ci gaba da luguden wuta a biranen uku da ke arewa maso yammacin Kyiv — Bucha, Hostomel da Irpin.
Ana ci gaba da gwabza kazamin faɗa a yankin. Dakarun Rasha sun harba rokoki kan fararen hula a Irpin a lokacin da suke ƙoƙarinrin tserewa, inda suka kashe wata uwa da yara biyu tare da raunata mahaifinsu.
An kuma tarwatsa wata gada ta wuccin gadi da mutane ke ratsa kogi domin tserewa daga ƙasar.