Labarai

Gobara : Later comer bala’i ne Matashi ya koka bayan wani yayi wuff da budurwasa

Advertisment

Wani matashi dan Najeriya wanda aka yaudara yana tunanin kawo karshen komai bayan budurwar da ya shafe shekaru uku yana soyayya da ita ta ci amanarsa.

Mawallafi Maazi Ogbonnaya Okoro ya wallafa hirar mutumin na Whatsapp a Facebook inda ya bayyana ainahin abun da ya faru.

Gobara : Later comer bala'i ne Matashi ya koka bayan wani yayi wuff da budurwasa
Gobara : Later comer bala’i ne Matashi ya koka bayan wani yayi wuff da budurwasa

Da yake martani ga hirar, Ogbonnaya ya nuna fushinsa kan abun da matashiyar ta aikata, yana mai cewa babu wanda ya cancanci irin haka imma namiji ko mace.legit na ruwaito

Chindera ta yi wasa da hankalinsa sosai

Advertisment

A hirar tasu, mutumin ya ce budurwarsa mai suna Chidera ta fada masa cewa yar’uwarta zata yi aure. Sai saurayin ya dauki budurwar tasa ya je ya yi mata siyayya a kasuwar Onitsha a ranar Talata da Laraba don shirya ma bikin.

Hakan ya kasance ne don budurwar ta fada masa cewa a ranar Juma’a za a yi bikin al’ada sannan a ranar Asabar a daura aure.

Bayan ya mata siyayya, ya kuma aikewa yar’uwar budurwar N50k sannan ya saka ta a mota don komawa gida a ranar Alhamis. Kawai sai ya gano cewa budurwar tasa ce zata yi aure.

Jama’a sun yi martani
Eziamaka Mma Okoye ya ce:

“Allah ya kyauta amma dai wannan jinsi nawa na da karfin hali faaa, ka dau hakuri dan uwana nima jinsinka na wahalar da ni da wasu mata masu soyayya ta gaskiya. a karshe duk za mu ji daidai.”

Nancy Ijeoma Silver ta ce:

Shekaru uku kacal, kawata wacce saurayin da suka shafe shekaru 9 suna soyayya ya yaudareta kuma ta ce me.
“Gaye ya auri budurwar da ya gabatar gaban kawata a matsayin abokiya kawai.
“Mallam dole rayuwa ta ci gaba, dukkanin jinsin ba nunawa junansu bakin hali. Ya kakkabe kansa sannan ya ci gaba da rayuwa.”

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button