Addini
AUDIO : Al’Kurani Da Matsayinsa ~ Dr Engr Bashar Aliyu Umar
Advertisment
Hudubar Juma’a daga Masallacin Alfurqan Kano daga Bakin Babban Limamin Masallacin Imam Dr. Bashir Aliyu Umar
Taken Huduba: Alqur’ani da Matsayinsa
Malam ya fara da cewa mu ji tsoron Allah, tsoron Allah itace wasiyyar Allah ga mutanen farko da mutanen karshe.
* Allah ya sanya Alqur’ani mu’ujiza ga Annabi (SAW)
* Allah ya kira Alqur’ani da sunaye masu yawa daga ciki akwai mai bada rayuwa, Annabi yace misalin wanda yake karanta Alqur’ani da wanda ba ya karantawa kamar rayayye ne da matacce.
* Allah ya sanya Alqur’ani littafi mai yawan albarka, albarsa tana fitowa a nan duniya, lokacin da mutum yake rayuwa da lokacin mutuwarsa, da lokacin da aka sanya shi a kabari.
* Abu Abdurrahmani Assulami ya zauna tsawon shekara arba’in yana karantar da Alqur’ani saboda Sayyadina Usman ya sanar da shi cewa Annabi yace wanda ya fi ku shi ne wanda ya koyi Alqur’ani kuma ya karantar dashi.
* Alqur’ani zai cece mutum a kabari, zan kange mutum daga azabar kabari.
* Alqur’ani zai zamanto abokin zama a kabari ga ma’abocin karanta shi.
* Alqur’ani zai roki Allah wasu abubuwa akan ma’abotansa, Allah kuma zai ba shi.
* Yana daga cikin albarkar Alqur’ani yana dauka matsayin hatta iyayen wanda yake karanta shi, bai tsaya ga wanda ya karanta ba.
* Mu kula da wannan littafi, shi ne darajarmu shi ne daukakarmu.
* Allah yana da mutanensa, ko kun san su waye wadannan mutane? Su ne ma’abota Alqur’ani.
* Alqur’ani shi ne zikirin da yafi komai daraja.
* Mu kula da masu koyar da Alqur’ani mu taimake su.
* Sarki Abdullahi tsohon Sarkin Makka ya bayar da babbar gona mai kimanin hectare 15 domin kula da ma’abota Alqur’ani.
* Mu kafa tsari, mu yi sadaqa, mu bada zakka ga ma’abota Alqur’ani domin. Kar mu wulakanta ma’abotansa ko masu karantar dashi.
* Sayyadina Umar yace Allah yana daukaka mutane da daraja albarkacin wannan Alqur’ani, haka nan Allah yana tozarta mutane da wannan Alqur’ani.
* Allah ya yi umarni da mu yi salati ga Annabi (SAW).
Allahumma Salli Ala Muhammad Wa Ala Alihi Sahbihi Ajma’in. Allah ka gafarta mana.
Allahumma Salli Ala Muhammad Wa Ala Alihi Sahbihi Ajma’in. Allah ka gafarta mana.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com



