Labarai

An Tsinci Gawar Wata Yarinya A Masallaci Bayan An Yi Mata Fyade A Jihar Kaduna

Daga Comr Abba Sani Pantami

An tsinci gawar wata karamar yarinya mai shekaru 6 a cikin wani Masallaci da ke jihar Kaduna bayan wasu kattai sun yi mata fyade har lahira, kamar yadda RFI Hausa ta ruwaito.

Lamarin ya auku ne a ranar Juma’ar da ta gabata a unguwar Kurmin Mashi da ke gefen babbar hanyar Nnamdi Azikwe a karamar Hukumar Arewacin Kaduna.

Jami’in hulda da Jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna, ASP Muhammed Jalige ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma ya ce kawo yanzu babu wanda aka cafke da ake zargi da hannu a aika-aikar, yayin da ‘yan sanda ke ci gaba da gudanar da bincike.

Masallatai a jihar Kaduna na ci gaba da kasancewa a rufe sakamakon dokar hana taruwar jama’a wadda aka kafa don hana bazuwar cutar coronavirus, yayin da aka gano gawar yarinyar da misalin karfe 3:20 na yamma a cikin Masallacin.

Matsalar fyade ta ta’azzara a ‘yan kwanakin nan a sassan Najeriya, abin da ya sa kungiyoyi daban daban ke kira ga mahukunta da su samar da dokar kashe duk wanda aka samu da aikata laifin fyaden.
Shafin rariya ya wallafa.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button