Labarai

Ina zaki Damu! Uba ya ɗirkawa ‘yar cikin sa mai shekaru 15 ciki bayan yayi mata fyaɗe

An cafke wani mutum mai shekaru 38 a duniya bisa laifin aikata fyaɗe ga ‘yar cikin sa mai shekaru 15 a duniya a jihar Ondo. Shafin LIB ya rahoto.

An cafke wanda ake zargin

‘Yan sanda sun cafke wanda ake zargin, Sunday Udoh, bayan yayi yunƙurin zubar da cikin da yarinyar ta samu bayan ya sadu da ita.

Udoh ya kai ɗiyar ta sa zuwa wani asibiti a Ile-Oluji, domin a zubar da cikin.

Sai dai, jami’an kiwon lafiya a asibitin sun sanar da jami’an tsaro bayan sun fahimci akwai rashin gaskiya a tattare da shi.

Hukumomi sun tabbatar da aukuwar lamarin

Da ya ke tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin hukumar ‘yan sanda ta jihar Ondo, SP Funmilayo Odunlami, ya bayyana cewa:

A ranar 26 ga watan Afrilun 2022, jami’an ‘yan sanda da ke a ofishin Ile-Oluji, sun amshi ƙorafin yunƙurin zubar da ciki da wani Sunday Udoh mai shekaru 38 yayi a wani asibitin a Ile-Oluji.

A yayin gudanar da bincike, an gano cewa wanda ake zargin yana yunƙurin zubar da cikin ɗiyar sa mai shekaru 15 wacce ya dinga saduwa da ita.

Kakakin hukumar ya kuma bayyana cewa zaa miƙa wanda ake zargin zuwa gaɓan kuliya bayan an kammala gudanar da bincike.

[Via] labarunhausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button