Naziru Sarkin Waka Yayi Raddi Mai Zafi Zuwa Ga El-Rufai Akan Kalamansa Na Cewa “A Cire Kayan Aikin Masu Fyade”
Idan baku manta a Nigeria ko ince a duniya ana samun labarai akan yaɗuwa yiwa yan mata fyade sosai wanda yan yara ƙanana har manya ba’a bari ba.
Shine anka samu shafin bbchausa ya wallafa mal nasiru El-Rufai ya ke cewa ” a cire kayan aikin masu fyade” wanda shine wannan shahararren mawakin hausa da sarakuna nazir m Ahmad yayi raddi mai zafi amma kuma akwai hikima sosai a cikinsa.
Ga jawabin sarkin waka.
“Idan mazakuta ake nufi??Wannan bai kamata ta fita daga bakin wanda yasan Allah ba… kuma addinin musulinci bai bada wannan damar ba hasali ma duk dokokin duniya basu bada ba.. bai kuma kamata muna fito da dokoki irin wannan ba? Duk tausanin ka ga bawa baka kai mahaliccin sa ba amma bai umarni da hakan ba, kuma duk son ka da a gyara baka kai manzo S. A. W. ba amma bai ce hakane yafi ba… kana so kace kafi Allah da annabi sanin mai ya kamata ne? Ya kamata ne ka kaddamar da shari’ar musulinci a garin Ka shine muka san kana so ayi gyara. Amma ana shaye shaye ana shirka ana yawo tsirara ba mu gyara ba… to meye zai gyaru? Mubi Allah kawai shine zamu ga dai dai… Allah yasa mu dace amin. KU SANI BABU WANDA YAFI KARFIN ZUCIYARSA SAI WAN DA ALLAH YASO”