Addini

Alkhairi Allah Ya kai Ga Bafarawa : Yadda Jami’ar Musulmi Zata Zamo Wanda Bafarawa Ya baiwa Kungiyar Izalah (A Cikin Hotuna)

Daga prof Mansur Sokoto
Alhamdu lillah, jiya Jum’ah mai tarin haske muka wayi gari da labari mai dadi na kataferiyar gudunmawar da Garkuwan Sokoto ya ba kungiyar JIBWIS ta ginanniyar Makarantarsa da ke Shinkafi don bunkasa ilimi da tabbatar da mafarkin kafa Jami’ar Musulunci hade da ilmoman zamani mallakar wannan kungiya. Aikin Makarantar ya kai wani mataki mai nisa kuma ya yi alkawarin kammala aikinta cikin watanni shida daga cikin aljihunsa. Wani abin ban sha’awa kuma ya ce, a sani ba shi da sauran bukata ga siyasa ta yin takara sai dai ra’ayi don kada a yi ma wannan sadaka tasa makauniyar fahimta ko bahaguwar fassara.
Garkuwan Sokoto Musulmin Najeriya muna godiya, Allah ya fi mu godewa.
Allah ya cika maka nufi na kammala wannan aiki a cikin lokacin da ka diba, ya yi ma sauran rayuwarka da dukiyarka da iyalanka albarka, ya jikan mahaifinka.
Babu shakka ka yi wa kanka dabara. Domin kamar yadda wani mai fasaha yake cewa:
*Komi yawan dukiyarka rabonka likkafani*
*Ayi ma hisabi kana kai dai cikin kabari.*
*Tunanina game da gudanar da wannan jami’a da dorewar ta:*
Gudanar da Jami’a a yanayin da muke ciki, kuma musamman a yankinmu na Arewa ba karamin abu ba ne. Musamman idan ana son ‘ya’yan bayin Allah talakawa su ci moriyarta.
Amma in da za a
A samu – domin fara gudanar da Jami’ar: Musulmi masu kishin samun nasarar ilimi da bunkasa ci gaban kasa su hada Naira biliyan daya abin zai yi sauki. Kuma abu ne mai yiwuwa kamar haka. A samu:
1. Mutane 12 da za su ba da gudunnawar N10m kowannensu = N120m
2. Mutane 20 da za su ba da gudunmawar N5m kowannensu = N100m
3. Mutane 100 da za su ba da gudunmmawar Miliyan 1 = N100m
4. Mutane 200 da za su bayar da gudunmawar N500,000 = N100m
5. Mutane 500 da za su bayar da gudunmawar N100,000 = N50m
6. Mutane 1000 da za su bayar da gudunmawar N50,000 = N50m
7. Mutane 20,000 su bayar da gudunmawar N5000 = N100m
8. Mutane 50,000 su bayar da gudunmawar N5000 = N250m
9. Mutane 100,000 su bayar da N1000 (Dubu daya kacal) = N100m
10. Mutane 50,000 su bayar da N200 kacal = N10m
11. Mutane 50,000 su bayar da N100 kacal = 5m
12. Mutane 150,000 su bayar da N50 = N15m
In da za a tara wadannan kudi a aljihun Kungiya kafin kammala aikin a cikin wata shida to, sauran zai yi sauki in sha Allahu.
Wannan ba mafarki ba ne. Abu ne mai yuwa, kuma kasashe da yawa sun gwada irin wannan sun ci nasara.
A yayin da nake kira ga al’ummar Musulmi su taimaka, ina kuma kira ga JIBWIS ta sake fito da wata sabuwar hanya tare da amfani da kafaifan watsa labarai da na sadarwar zamani (Social Media) domin tabbatuwar hakan.
Tafiyar Kilomita 1000 da tako daya ake fara ta.
Dan uwa, duba ka gani. A cikin wane daga cikin goma sha biyun nan Allah ya ajiye ka? Yi kokari kada ka yi kasa da matsayinka.
Mu ba Allah, Allah ya maida mana da mafifici.
Allah ya tabbatar da wannan kuduri na alheri, ya ba mu ikon taimakawa.
Ga dai Akawun din Kungiya wanda ta ware don wannan muhimmin aiki:
*ACC. NAME*: JIBWIS AS-SALAM INT’L UNIVERSITY
*ACC. NUMBER:* 0006027065
*BANK:* JAIZ BANK
*SORT CODE:* 301080169

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button