Kannywood

INNA lillahi wa inna ilaihir raji’un! Allah ya yi wa mahaifin jaruma Hajara Isah Jalingo rasuwa

Advertisment

INNA lillahi wa inna ilaihir raji’un! Allah ya yi wa mahaifin  jaruma Hajara Isah Jalingo rasuwa a daren jiya.

Malam Isah Tidwa Jalingo ya rasu a daren Alhamis, 30 ga Afrilu, 2020, a ‘Federal Medical Centre’ da ke Jalingo, babban birnin Jihar Taraba, bayan doguwar jinya da ya yi fama da ita.

Hajara ta faɗa wa mujallar Fim cewa mahaifin nata ya yi fama da rashin lafiya, yau da lafiya gobe ba lafiya.

Kwana biyu da su ka wuce har sai da numfashin sa ya fara ɗaukewa, sai da aka sa masa na’urar numfashi (ventilator).

Marigayin ya rasu ya na da kimanin shekara 67 a duniya, kuma ya bar ‘ya’ya 15.

Allah ya sa mutuwa hutu ce a gare shi, amin.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button