Ganduje Ya Bayyana Abin Da Yasa Ya Roki Buhari Ya sassauta Dokar Hana fita a Kano
Gwamnan jahar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana dalilan da suka sa yake rokon gwamnatin shugaba Buhari ta sassauta ma jama’an Kano dokar hana fita da ta kakaba musu.
Daily Nigerian ta ruwaito a ranar Alhamis ne Ganduje ya yi wannan kira yayin da yake rantsar da wani kwamitin kwararru da za su taimaka ma kwamitin yaki da COVID19 na jahar Kano.
A jawabinsa, Ganduje ya roki Buhari ya rage kwanaki 14 da ya sanya ma jahar Kano na ba shiga ba fita, saboda a cewarsa hakan zai rage wahalhalu a jahar, musamman a watan Ramadan.
“Za mu zauna da kwamitin yaki da COVID19 na shugaban kasa don neman izinin sassauta dokar ta bacin da aka sanya ma Kano, muna wannan kira ne a madadin jama’anmu wanda a yanzu haka abincinsu ya kare.
“Muna kira ga gwamnatin tarayya ta sassauta dokar na dan wani lokaci don jama’a su samu daman sayen abinci, musamman a yanzu da yawancin mu suke azumi, hakan zai rage radadin da ake ciki.” Inji shi.
Sai dai a wannan rana da Ganduje yake wannan roko, sai ga shi an samu karin mutane 80 da suka kamu da cutar Coronavirus a jahar Kano, wanda ya kawo jimillan masu cutar zuwa 219.
A wani labari kuma, Gidauniyar Kwankwasiyya, ta Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ta bayyana damuwarta bisa yadda gwamnan Kano, Ganduje ya yi biris da kyautar da ta baiwa jahar.
Kimanin kwanaki 10 da suka gabata ne Kwankwaso ya sanar da bai wa gwamnatin jahar Kano kyautar wani asibiti da ya gina mai suna Amana domin a dinga killace masu cutar Coronavirus.
Asibitinyana nan ne a kan titin Miller, kuma yana cin gado 30 ne, kamar yadda kaakakin dan takarar gwamnan Kano a PDP, Abba Yusuf, Ibrahim Adam ya sanar a ranar 20 ga watan Afrilu.
Sanawar ta kara da cewa asibitin na cike ne da kayan aiki, wadanda Kwankwaso ya sanya a ciki tun zamanin da yake majalisar dattawa.