Labarai

ƘILU TA JA BAU: Miji ya kashe matarsa kan Ƙin Dafa masa abincin Sahur

A yayin da kowa yake kokarin ganin ya samu dacewa a cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana Sai gashi wani mutumi ya kashe matarsa da suka yi aure shekaru biyu da suka wuce akan taki dafa masa abincin sahur.

Mutumin dai yayi amfani da bindiga ya harbe ta ne har lahira kamar dai yadda mahaifin yarinyar ya yiwa ‘yan sanda bayani, Watan Ramadana wata ne da ake so kowa ya roki gafarar ubangiji, amma duk da haka muna abubuwa kamar dabobbi, wannan wani labari ne dai zai sanya mutane su dinga mamakin halayyar dan adam.

Lamarin dai ya faru ne a Khyber Pakhtunkhwa
Matar na da shekaru 19 kacal a duniya, tayi aure shekaru biyu da suka wuce. Bayan gabatar da bincike an gano cewa mijin ya kashe matar ne saboda taki dafa masa abinci.

Daga baya ‘yan sanda sun kama mutumin. A cewar uban yarinyar mijin dan gidan dan uwanshi ne, ma’ana dai kamar da ne a wajenshi.

“Mahaifin yarinyar yana yin alwala yana shirin yin sallar Asuba, kawai sai jin harbin bindiga yayi daga dakin ma’auratan,” cewar jami’in dan sanda.

“Da yaje domin ya duba abinda ke faruwa, sai ya tarar da ‘yarshi kwance cikin jini, inda tuni har mijin ya gudu,” dan sandan ya kara da cewa.

Abinda ya faru ya riga ya faru dai, ba wai kuma iya kashe ta da yayi bane, shima zai zo ya kari rayuwarshi a gidan yari.

A matsayinmu na Musulmai dole ne muyi koyi da sunnar manzon mu Annabi Muhammadu (SAW), shine abin koyi ga kowanne Musulmi na duniya. Idan har zamu dinga karanta tarihin yadda Annabi yayi rayuwarsa da matansa duk irin haka baza ta faru ba.

Madogara facebook/ Jaridar Dimokuraɗiyyar

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button