Shugaba Tinubu ya yaudare mu da karin kudin man fetur-NLC
Kungiyar Kwadago ta kasa NLC ta ce shugaban kasa Bola Tinubu yaudari ’yan kwadago, ta hanyar kara farashin mai.
Kungiyar kwadagon ta bayyana cewa a tattaunawar da kungiyar tayi da gwamnatin a kwanakin baya ta amince da naira 70,000, shugaba Tinubu ya bayar da zabin kin kara farashin man fetur.
Shugaban kungiyar ta NLC, Joe Ajaero, ya bayyana haka a lokacin bude taron yini biyu a Legas mai taken “Bita kan mafi karancin albashi.
Ajaero ya ce an yi yunkurin dauke hankalin kungiyar kwadago tare da zargin laifi da tallafawa ayyukan ta’addanci tare da daukar nauyin ta’addanci da sauran su.
Dclhausa ta ruwaito cewa, Ajaero ya bayyana cewa tsadar man fetur a halin yanzu ya durkusar da karin mafi karancin albashi na naira 70,000 da har yanzu ba a fara aiwatar da shi ba, inda ya bukaci gwamnati da ta gaggauta magance matsalolin yunwa da fatara da suka addabi ‘yan Nijeriya.
Ajaero ya bayyana tattaunawar da suka yi da Tinubu gabanin amincewa da mafi karancin albashi na N70,000, inda ya bayyana cewa a tattaunawar da ake yi, Tinubu ya bayar da zabin karbar albashin N70,000 ba tare da karin farashin man fetur ba.
Ajaero ya ce kungiyar kwadago ta zabi naira 70,000 duba da irin mawuyacin halin da za a shiga da karin farashin man fetur idan har ma’aikata za su sasanta kan albashin N250,000.
Ya kara da cewa saboda a kautar da hankalin kungiyar yasa aka bijiro musu da wasu zarge-zarge domin gwiwoyin su suyi sanyi.
Ya sake nana ta cewa shugaban kasa ya ci amanar su, wannan sanarwar da suka fitar a kwanaki jami’an gwamnati suka karyata suna kan bakan su.