Bazamu Yarda Mu zura Ido Ana Satar Mutane Har Gida Ba – Gwamna Zulum
Kamar yadda BBCHausa suka hada rahoton, Maigirma Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum yace: “Ba za mu yarda yaƙin satar mutane har gida ya ci mu ba..”
Farfesa Babagaba Umara Zulum (Khadimul Ummah) yace dole ne a tashi tsaye domin daukar matakan da suka dace kan masu satar mutane har gidajensu
Gwamna Zulum ya yi wannan bayani ne a yayin taron ƙungiyar gwamnonin arewa maso gabashin ƙasar karo na uku da yake jagoranta
Zulum ce ganin yadda wannan matsala ke ta’azzara wadda kuma tuni ta yi ƙamari a johohi irinsu Kano da Kaduna, akwai buƙatar kungiyar tasu ta ɗauki matakin daƙile wannan mummunan aiki karya ƙarasa yankinsu.
Ya ce a matsayinsu na gwamnonin da al’umma suka bai wa yardarsu, dole ne su samar da aminci ga matafiya daga jiha zuwa wata, ya nemi kuma kwamitin kwamishinonin shari’ar yankin da su samar da tsarin shari’a da zai tunkari wannan annoba na garkuwa da mutane
Ya kuma yi bayani game da abin da ke ƙara addabar mutane a ƙasar baki ɗaya,wato matsalar fyaɗe, ya ce dole ne a lalubo hanyar da za a kare mata tare da basu ƙarfin gwiwar yin rayuwa kamar kowa.
Cikin matsalolin da aka tattauna a kwai maganar Boko Haram da kuma maganar kan Almajirci da fatan ganin an kawo ƙarshen shi ta hanyar da ta dace
Jama’a kunga wannan shine tsarin shugabanci na gari, wato daukar mataki tun kafin barna ta iso
Allah Ka taimaki Gwamna Zulum Khadimul Ummah