Cigaba Yazo : Za a Haska fim Din Kannywood A Amurka
Mashirin fim din Jalil ya bayyana cewa sun shirya tsaf domin haska kayataccen fim dinsu mai suna Jalil a Jihar Atlanta da ke Arewacin Amurka. Inda mu kuma Hausaloaded mun samu daga jaridar Aminiya.
Jarumi Yakubu Mohammed, wanda ke daya daga cikin jaruman fim din ne ya bayyana haka a shafinsa na Instagram.
Yakubu Mohammed wanda ake kira da Yakx ya ce, “Za a kaddamar da fim din Jalil a Plaza Theatre da ke Atlanta a ranar 22 ga watan Maris. Wannan ne karo na farko da za a kaddamar tare da haska fim din Kannywood a Arewacin Amurka.”
Shi ma mashiryin fim din, Lesli No’iless Dapwatda, wanda mashiryin fim ne a Amurka ya bayyana cewa ya ji dadin fim din, sannan ya bayyana godiyarsa ga jarumai da suka taka rawa a fim din irinsu Yakubu Mohammed da Maryam Booth da Ali Nuhu da sauransu.
“Wannan duk kokarinku ne. Ina fata za ku kasance tare da mu a Atlanata domon kallon fim din.” Kamfanin shirya fina-finai na Noless Studio da ke Atlanta ne ya dauki nauyin fim din ya zimmar bayyana al’adun Afirka.
Join Our WhatsApp Channel
Get verified job vacancies, career tips, scholarships and opportunities delivered straight to your phone, free and as soon as they're posted.



