Kannywood

Idan Adam A Zango Ya Shigo Kano Sai Mun Kama shi – Hukumar Tace Fina Finai – Afakallahu

Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano Malam Isma’il Na Abba Afakallahu ya jaddada aniyar sa ta cewa muddin jarumin Finafinan Hausa Adam A. Zango ya shigo garin Kano sai Hukumar ta yi ram da shi.
Hakan ya biyo bayan wata sanarwar jarumin da aka gani a shafin jarum Rahama Sadau a  Instagram, inda aka ga Zango yana sanar da masoyan sa cewa zai shigo garin domin kallon sabon shirin nan mai suna ”Mati A Zazzau” wanda ake nunawa a Film House Cinema Kano.
A bidiyon jarumin ya kira ga masoyan sa, da su hadu da shi a ranar Lahadi da kuma ranar Litinin domin kallon shirin tare da shi.
Wani bayanan sirri da kafar watsa labarai ta ‘Kannywood Exclusive’ ta samu shi ne, Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta gama shirin ta na musamman domin kama jarumin muddin ya shigo silimar wurin kallon shirin, kasancewar jarumin ya ki yin rijista tare da bin sauran ka’idojin hukumar.
Da ya ke yi mana karin bayanin game da zargin da ake yi wa hukumar na shirin kama Zango, shugaban Hukumar Malam Isma’il Na Abba Afakallahu ya ce, Kano ta na bambancin da sauran jihohin Arewa. Sannan hukumar tace Finafinai an kafata ne domin tsaftace addini da kuma al’adar jihar Kano.
Don haka duk mutumin da ya yarda zai girmama al’ummar Kano dole ne ya bi dokokin su wanda majalissa ta tabbatar da su tun a shekarar 2001.
.
Afakallahu ya ci gaba da cewa, duk mutumin da bai yarda harkar fim hanya ce ta sadarwa da za ta haskaka addini da al’ada ba ta yadda mutanen Kano suke, ko wanene shi mun hakura da shi ko da kuwa kyamara ce ta haife shi.
Shi wannna jarumin ya yi bayanin cewa ba zai yarda ya bi wannan ka’idoji ba, kuma ba zai girmama su ba, to mene ne zai nunawa mutanen Kano da har zai cewa masoyan sa su yi gangami, me ya ke da shi da zai gabatar akan su?
Dokar mu ita ce, duk mutumin da bai yi rijista ba, babu wani abu da zai taso na jihar Kano ya zo yace zai yi mu kuma mu zuba masa ido mu kyale shi bai isa ba, ko ma wanene.
Shi daman ya ce babu ruwan sa da Kano, to ka ga kenan bai da hurumin da zai shigo ya yi wani abu da hukuma ta ke da hurumi da shi. Ba shi ba, ko wanene ya ce zai zo in dai ba zai bi doka ba, ya yi tsararo kuma ba za mu kyale shi ba.
Kannywood duk abin da ake yi ta yi masa, amma tun da yace, babu ruwan sa da Kano, to mu ma babu ruwan mu da shi.
Sai dai jarumi Adam A. Zango ya bayyana cewa maganar da ake yadawa game da cewa shi babu ruwan sa da mutanen Kano, babu komai a cikin maganar illar kanzon kurege.
A cewar sa, an ce na bar Kannywood, na fada ba karya na yi ba, na bar Kannywood. Na yi bidiyo kuma na yi rubutu a shafukana na sada zumunta. Ni yanzu jarumi ne mai cin gashin kan sa a karkashin kamfanina wanda na yi wa rijista.
Maganar cewa babu ruwana da Kano, wannan maganar teburin mai shayi ce, domin babu wanda ya ke da shaidar na fadi ko na rubuta a wani wuri, idan kuma akwai shi a nunawa duniya ta gani.
Kawai so ake a hadani da masoyana na jihar Kano, shi ya sa ake kirkirar wasu abubuwan don a lika mani bakin jini.   Amma har yanzu masoyana na Kano karuwa suke.
Don haka ina so bai wa masoyana na jihar Kano hakurin cewa ba zan samu damar zuwa kallon fim din ba kamar yadda na yi bayani.
Ba don komai ba sai don in zauna lafiya, ina da iyali da kuma wadanda na ke taimaka mawa, idan suka kamani za su wulakanta ni, domin bani da gata sai Allah.
Idan hukumar tace Finafinai ta haramta mani zuwa Kano, sai in je sauran jihohin da mu ke da su a Nijeriya, duk da dai bani inda na ke so kamar Kano, saboda da su na samu daukaka, amma yau an yi min iyaka da garin.
Kuma wannan kulli ne tare da hadin gwiwa da wasu ‘yan cikin masana’anatar fim da suke so su ga bayana.
Tun a lokacin wasan babbar sallah su ka so kamani Allah ya tsallakar da ni. A wancan lokacin ni ne kawai dan wasan da aka ce sai ya yi ”Clearance” har da wadanda ba ma addinin mu daya ba, amma sun zo sun yi wasan su a Kano, lami lafiya, ni kuma aka hanani.
Ko a wurin kallon Finafinan da ake haskawa a Silima, akwai wadanda ba su da rijista da hukumar tace finafinai, irin su mawakiya “Dija” wadda a Legas ta ke zaune, ta zo ta kalli fim din ta yi hotuna da masoyan ta, ta koma gida lafiya, amma sai ni aka kafawa wannan dokar.
Amma ina so a sani komai lokaci ne, sannna babu wanda ya isa ya hanani shigowa Kano, domin ina da ‘yan uwa da abokan arziki wadanda na ke kawowa ziyara ko ba don harkar fim ba. Su kuma wadanda suka hada baki da wannan hukumar domin su ga bayana, ina so su sani, in-sha Allah ba za su taba ganin wannna ranar ba.
Kannywood Exclusive
14-02-2020

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button