Labarai

WATA SABUWA: Budurwar Suleman Tace Umma Ta Gaida Assha

Advertisment

Daga Nasiru Salisu Zango

Nafisa Tahir itace budurwar matashin nan Suleman wanda Ba Amurkiya Jeanin Sanchez ta yowa tattakin  soyayya tun daga Amurka ta kuma bashi zoben kauna tare da shirin yin aure,Kuma ga alama shaukin soyayyar baturiyar ya jefa shi  cikin tekun kauna har takai ya mance da tsohuwar zumar sa Nafisa.

A hirar mu da Nafisa tace Sam abin Bai wani dame ta sosai ba, murna ma tayi ganin cewar an yi yunwa halin kowa ya fito Dan haka tace tana yiwa Suleman da sabuwar masoyiyarsa fatan alheri.

Tace ta godewa Allah da Jeanine ta bayyana da wuri har takai abin boye ya fito fili.

Anasa bangaren mahaifin Suleman Malam Isa, yace bashi da sauran shakku akan auren dansa da sabuwar masoyiyarsa domin ya lura mutuniyar kirki ce me ladabi da biyayya, yayi musu fatan alheri a wannan aure wanda yace babu wata matsala tun da suna kaunar juna.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button