Labari mai dadi : Tinubu zai bada tallafi dubu hamsin 50k ga mutane
A yanzu nan majiyarmu ta samu wata sanarwa wanda ta fito daga mai bada shawara ta musamman akan harka labarai a kafafafen yanar gizo Abdulaziz Abdulaziz kamar yadda shafin Rabiu Biyora ya wallafa a shafinsa kamar haka.
“Mai girma Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu zai bayar da tallafi na naira 50K ga mutane 1,300 a fadin ƙananan hukomomi 774 dake fadin Najeriya.
Sannan za’a bawa masu kananen sana’oi bashin dubu 500k zuwa Mliyan daya 1m. Zaku ma a bawa masu manyan Jari suma bashi na kudade masu yawa duk dan su bunkasa harkokin su.
Wannan yana cikin kokarin gwamnati Tarayya na bunkasa tattalin Arzikin Kasa da kuma ragewa mutane radadi na yanayin da ake ciki.
Abdulaziz Abdulaziz
SSA PMedia.”.
Fatan mu wannan shirin Allah yasa ya amfani talaka da talakawa kada yan siyasa suyi sama da fadi akan wannan tallafi.