Labarai

Janet Jackson da Chris Brown da 50 Cent sun cashe a Saudiyya (Hotuna)

Advertisment

Fitattun mawaka da makadan Amurka sun cashe a birnin Jeddah na Saudiyya, bikin casu da ‘yan kasar suka dade suna jira.

An gudanar da gagarumin bikin casun ne a dandalin Sarki Abdallah a birnin Jedda, kuma daga cikin mawakan da suka cashe sun hada da Janet Jackson, 50 Cent da Chris Brown.
Wannan shi ne bikin casu na farko da aka taba gudanarwa a kasar Saudiyya.

Dandazon ‘yan kallo sun yi ta shewa cikin annashawa da yanayin nan na ba-sa-ban-ba, saboda shekaru biyu da suka gabata idan aka ce za su samu dama irin haka ba za su amince ba.
Baya ga fitattun mawakan Amurka an kuma gayyato fitattun mawakan Larabawa kamar Tamir Husny da Muhammad Abdou da sauransu.

Hotunan da aka yada a kafafen sadarwa na Intanet sun nuna Janet Jackson da tawagarta sun yi shiga ba kamar yadda aka saba gani ba ta tsaraici dukkaninsu sanye da bakin tufafi.

Advertisment

An yi casun ne ba tare da Nicky Minaj ba, wacce ta sauya ra’ayi bayan gayyatarta saboda damuwa da ‘yancin mata da masu luwadi da madigo a Saudiyya.
Ko da yake Jaridar Okaz ta gwamnatin kasar ta ce ba Nicky ce ta janye bisa radin kanta ba, Masarautar Saudiyya ce ta sanya ta hakan saboda yadda ake ta sukar lamirinta.

A baya-bayan nan dai kasashe daban-daban sun matsawa Saudiyya lamba kan batun take hakkin dan adam da ‘yancin fadar albarkacin baki.
Wannan ya biyo bayan kisan dan jarida kuma dan kasar Jamal Khashoggi wanda ya yi kaurin suna wajen sukar masarautar kasar da Yarima mai jiran gado Muhammad bin Salman al-Saud.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button