Magidanci Ya Yi Wa Yara Goma Fyade Ta Hanyar luwadu A Garin Marrraba/Nyaya (hotuna)
An gurfanar da wani magidanci mai suna Adamu Umar Dunomo mazaunin Unguwar Rugar Juli dake yankin Mararrabar Abuja a karamar Hukumar Karu dake jihar Nasarawa a gaban babar kotun Majistare dake kasuwa Mahammadu Buhari International Market Mararraba bisa zargin aikata laifin fyade ta hanyar Luwadu ga kananan yara maza su goma masu kimanin shekara 4, 7, 10, 12 binciken mu ya tabbatar da duka yara basu haura shekara 17 ba.
Shafin Rariya kamar yadda ya ruwaito,dan sanda mai gabatar da kara Mr. Nanzi ya fara gabatar da qanda ake zargi da aikata laifin ranar 31 ga watan Agustan 2020, daga nan kotu ta ajjiye shi a Gidan yarin suleja har zuwa ranar litinin 28 ga watan Satumbar 2020 inda aka samu akasin kawo wanda ake zargin kotu a makare har aka tashi.
Wasu daga cikin iyayen yara da aka yi wa fyaden da Shugaban mazauna unguwar Alhaji Aliyu Ahmad Janyau, sun yi kira ga kungiyoyi masu zaman kansu da uwargidan Gwamnan jihar Nasarawa Hajiya Salifat Abdullah A. Sule da su shigo lamarin dan tabbatar da an hukunta mai laifin
Alkalin kotun Mai Shari’a Hauwa Onu Osa, ta dage sauraron sauraron karar zuwa Litinin 26 ga watan Oktoban 2020.