Kotu ta dakatar da karya belin Muaz Magaji
A yau Litinin ne shari’ar Muaz Magaji Ɗan-Sarauniya ta ɗauki wani sabon salo, bayan da Kotun Majistare 58 ta dakatar da karya belin da ta bashi kwanakin baya.
Tun da fari, a yau ɗin kotun ta karya belin da ta baiwa Ɗan-Sarauniya ɗin sakamakon ƙin halartar kotu da ya yi, daga bisani kuma sai ta janye karya belin ba da daga bisani ya halarta.
A ranar juma’a, tun safe Magaji ya je kotun, ya yi ta jira har zuwa da rana, amma da ga bisani sai alƙalin ya shaida wa jami’in kotun cewa ba zai samu damar zama ba.
Sai kotun ta sanya yau Litinin da karfe 2 na rana bayan bikin Kungiyar Lauyoyi ta Nijeriya, NBA domin ci gaba da shari’ar, amma kuma sai kotun ta zauna da misalin ƙarfe 1 na ranar.
Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa bayan da karfe 2 ta yi, sai ga Magaji da lauyansa Gazzali Ahmad, inda a ka shaida musu cewa tuni kotun ta zauna kuma har ta janye ma belin da ta bashi.
Daga nan ne sai lauya Magaji ya ƙalubalanci matakin na kotun, inda ya ce shi wanda yanke karewa ya zo ƙarfe 2 daidai kamar yadda a ka faɗa musu a matsayin lokacin zaman kotun.
Bayan ya saurari ƙorafin na kayan Magaji, da ga bisani sai alƙalin, Aminu Gabari ya janye karya bekin da kuma umarnin kamo Magaji.
Daily Nigerian Hausa ta tuno cewa kotun na tuhumar Magaji ne da laifukan da su ka shafi yarfe, cin mutunci, ƙage da kuma tada tarzoma a kan Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje.
Laifukan sun saba da sashi na 392, 399 da 114 na kundin dokar laifuka ta 1999.
Daga bisani kotun ta bada belin Magaji, shahararren ɗan adawar Ganduje, na Naira miliyan 1.