Duk wanda yace an yiwa Annabi sihiri a kashe shi – Sheikh Abubakar Mahmud Gumi
Marigayi Dr. Abubakar Mahmud Gumi a wani tafsiri nashi ya bayyana cewa duk wanda ya yadda cewa an yiwa annabi sihiri hukuncin shi kisa
– Malamin yayi tsokaci akan irin kariyar da Allah ya ce zai bai wa Al’kur’ani Mai Girma, inda ya bayyana cewa babu wani littafi a duniya da ba canja shi ba sai Qur’ani
– Ya ce shi bai taba yin wata magana da ta nuna cewa ya ce an yiwa Annabi sihiri ba, kuma duk wanda ya yarda da haka hukuncin kisa ne a kanshi
A wani tafsiri da Marigayi Sheikh Dr. Abubakar Mahmud Gumi (Allah ya gafarta masa) da jimawa an jiyo muryar Malamin yana magana akan hukuncin wanda ya ce an yiwa annabi sihiri.
Shahararren Malamin ya ce, “Kowanne littafi dake duniyar nan da an bugo shi za a iya canja shi, amma banda Al’kur’ani Mai Girma saboda shine littafin da Allah yayi alkawarin tsarewa.
“Allah bai yi alkawarin tsare Bukhari, Muslim da sauransu ba, saboda yana yiwuwa wasu su kara, saboda haka ku auna Al’kur’ani, ku je kuyi ta bincike.
Wata tambaya da wani mai sauraron wa’azin ya yiwa Malamin, Sheikh Gumi ya bashi amsa da cewa, “Ka taba jin inda nayi magana akan cewar an yiwa Annabi sihiri? Ko ka san inda aka yiwa Annabi sihiri?
“Ni nayi magana akan Bukhari da Muslim ne, wanda ya yarda an yiwa Annabi sihiri sai kisa.” In ji Malam.