Ki dunga Jan Hankali maigidanki Idan kun zo wajen kwanciya – Obasanjo Ga Aisha Buhari
Tsohon Shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo yace uwargidar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha, tayi namijin kokari da ta bayyana gazawar gwamnatin maigidanta
– Obasanjo ya bukaci Aisha da ta dunga tadi da maigidan nata idan sun zo kwanciya don jan hankalinsa akan abubuwan da ke wakana a kasar
– A kwanan nan ne Aisha ta caccaki shirin bayar da tallafi na gwamnatin tarayya da kuma tsarinta na magance lamarin ta’addanci a yankin arewacin kasar Tsohon Shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo yace uwargidar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha, tayi namijin kokari da ta bayyana wuraren da gwamnatin maigidanta ta gaza.
A kwanan nan ne Aisha ta caccaki shirin bayar da tallafi na gwamnatin tarayya da kuma tsarinta na magance lamarin ta’addanci a yankin arewacin kasar. Don haka a ranar Litinin, 3 ga watan Yuni, Obasanjo ya bukaci Aisha da ta dunga tadi da maigidan nata idan sun zo kwanciya a matsayin hanyar jan hankalin Shugaban kasar domin sanar dashi rashin jin dadinta akan abubuwan da ke wakana a kasar.
A wani jawabi daga hadiminsa, Kehinde Akinyemi, Obasanjo yayi maganar ne lokacin da ya taka rawar mai masaukin baki na hukumar tantancewa na wata kafar sadarwa, wato Penpushing Media a dakin karatunsa na Abeokuta.
Majiyarmu tat samu wannan daga jaridar legit.ng/hausa a jinjina wa uwardidar Shugaban kasar, cewa matsayarta abune mai kyau ga ci gaban kasar.

![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)





