Labarai
Ina karanta littafin wani Bature kan zaben sabon Sarkin Zazzau – El-Rufa’i
Advertisment
Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya ce yayin da ya ke jiran sunaye daga masu zaɓen sarkin Zazzau, yana karanta wani tsohon littafi na wani Farfesa farar fata kan zaɓen sabon sarkin Zazzau.
A shafinsa na Twitter, El-Rufa’i ya wallafa hoton bangon littafin da Farfesa M G Smith ya rubuta mai taken “Gwamnati a Zazzau.” wanda aka buga a 1960.
Gwamna El- Rufa’i ya ce littafin da ke bayani kan zaɓen sarakunan Zazzau daga 1800 zuwa 1950 zai masa jagora wajen yanke shawarar zaɓen sabon sarkin Zazzau, tattarawa bbchausa
KADUNA UPDATE: While awaiting the recommendations of the Zazzau Emirate kingmakers, I am re-reading Prof M G Smith’s authoritative epic on the selection of Zazzau Emirs from 1800 to 1950 to guide me in taking a decision. “Government in Zazzau” was published in 1960. – @elrufai pic.twitter.com/h4sgPlUvXw— Nasir Ahmad El-Rufai (@elrufai) September 24, 2020
Advertisment
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Masha allahu Allah