Labarai
Next Level: Zahra ta yi rubutu mai ratsa zuciya zuwa ga Buhari
Advertisment
– Diyar shugaba Muhammadu Buhari, Zahra ta yi murnar fara mulkin mahaifinta zango na biyu – Zahra ta yi addu’ar zango na biyun ya fi na farkon alheri
– Ta taya mahaifinta murna a kafar sada zumunta inda ta ce Allah ya sake bashi damar jagorantar Najeriya cikin adalci da gaskiya Zahra Buhari, daya daga cikin ‘ya’yan Shugaba Muhammadu Buhari ta yi amfani da kafar sada zumunta domin murnar fara mulkin mahaifinta karo na biyu.
Ta yi rubutu mai ratsa zuciya ga mahaifinta a shafinta na Instagram. A cikin rubutun, ta bayyana cewa Allah ne ya sake bawa mahaifinta ikon ya yiwa Najeriya jagoranci na adalci.
Ta kuma yi addu’ar cewa abubuwa za su fi canja a wannan zangon na biyu. Ta yi fatan za a biya wa ‘yan Najeriya bukatunsa sannan masu rike da mukamman gwamnati su mutunta ‘yan Najeriya ta hanyar yi musu aiki tsakaninsu da Allah kuma ‘yan Najeriya sune canjin da ake bukatar a kasar.
munSamu wannan labari ne daga Legit.ng ta ruwaito cewa ‘yan Najeriya sunyi murnar rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari kan mulki zango na biyu. ‘Yan kasar sun yi ta yada hotunnan shugaban kasar yayin taron rantsuwar kama aiki da akayi a dandalin Eagle Sqaure da ke birnin tarayya, Abuja.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com