Labarai

Waccan fatawar ta Malam Ibrahim Khalil ta kusa kama da halarta shan taba – Muhsin Ibrahim

A dokar duniya ana rubuta cewar “ma su shan taba za su mutu da wuri” ko makamancin haka a kwalinta. Ma su shan taba sukan ƙaryata wannan kashedin. Dalili kuwa shi ne: wasu mashaya sigari sukan tsufa suna shan abarsu, marasa sha kuma sukan mutu da wuri.

Don haka, duk da cutar da take cikin sigari, idan wani ɗan takifen likita ya ce maka sigari ba za ta kashe ka da wuri ba, shi kenan sai kai ta sha!

Amma fa hatsarin fatawar can ta fi haka. Ko a psychology, yawanci wanda yake “bleaching” yana da matsala. Yana ganin ƙasƙanci a yadda Allah ya yi shi ne. Kuma idan suka fara, ba sa iya dainawa. Bal, idan ma ka daina lalacewa fatarka take yi.

Gaskiya bai kamata malamai su buɗe irin wannan ƙofar ba. Malam Aminu Daurawa ya taɓa cewa ƙarin gashi ga mace don ta birge mijinta ba laifi ba ne — ko wata magana irin wannan. Duk da ya ƙara bayani daga baya, kana magana a yau sai yarinya ta ce Malam ya halatta. Yanzu saka “wig” ya zama “normal”!

Kafin wani ya zage ni, ni ba malami ba ne. Sai dai gyara ko jan hankali irin wannan ba aikin malamai ba ne kawai. Bleaching abu ne MARA KYAU — medically, psychologically, socially, even rationally.

Allah ya sa mu gane mu kuma gyara, amin.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button