Kannywood

Wata sabuwa ! An Kwantar Da Amina Amal Saboda Dukan Da Gabon Tayi Mata

JARIDAR DIMOKURADIYYA: Rahotanni sun tabbatar da cewar yanzu haka Jaruma Amina Muhammad Amal, ta kwance share share bata da lafiya tun bayan da Jaruma Hadiza Gabon tayi mata dukan tsiya da Belt.

Rahotannin sun bayyana cewar Amina Amal tana cikin yanayin firgita da dimuwa har ila yau ga zafin jiki, yanzu haka tana kwance.

A yanzu haka Amal ta bar Kaduna, saboda hatsarin da rayuwarta ke ciki bisa hasashen za a iya daukar nauyin ‘yan ta’adda su sake kai ma ta hari. To, amma jim kadan bayan hakan sai ta kwanta jinya sakamakon barazanar da ta fuskanta, inda yanzu haka likitoci na kokarin ceto rayuwarta ne, saboda a na kyautata zaton cewa, lamarin ya haifar ma ta da ciwo a zuciyarta.

Idan baku manta ba a a makwan daya gabata ne aka ga Jaruma Hadiza Gabon tana dukan Amal da Bulala,  bisa zargin ta da bata mata suna da kuma alakanta ta da Yar madugo.

A daren ne masu kai farmakin su ka tafi da wayar yarinyar. Daga nan ne fa bayan Amal ta farfado ta nemi da a dawo ma ta da wayarta, amma sai ita Gabon ta ba ta sharadin cewa, sai dai ta zo ta dauke ta a bidiyo ta na ikirarin cewa sharri ta yi ma ta, kafin ta mayar ma ta da wayar. Wannan ya kai ga a ka ga Amal a wani bidiyon ta na karyata kanta, don kawai ta amshi wayarta.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button