Kannywood

Allah Ba Zai Kyale Ku Ba Karnukan Farauta – Daga Datti assalafiy

Ni banga wani banbanci tsakanin Hadiza Gabon da kuma Amina Amal ba, idan akwai banbanci a tsakaninsu ni dai ban sani ba

Na kalli video na biyu wanda Hadiza Gabon ta killace Amina Amal a cikin wani daki tana ta falla mata mari sai kace ‘yar cikinta, naji Hadiza Gabon tana ta kiran sunan wani Ustazu da yake kokarin bata hakuri, ko me ya kawo ustazu kusan da wadannan annoba oho!? anya kuwa ustazun gaskiya ne?

Wato duk alakar Hadiza Gabon da manyan ‘yan siyasa da kuma ‘yan boko ace sun kasa bata shawara ta aikata wannan danyen hukunci, kwatsam sai na samu labari masoyan Amina Amal sun daukar mata lauyoyi sun maka Hadiza Gabon a kotu

Babu shakka Hadiza Gabon bata san dokokin Nigeria ba, abinda ta aikata manyan laifuka ne a Nigeria, ta aikata laifukan zargi har guda uku, na farko za’a zargeta da yin garkuwa (Kidnapping/Abduction), na biyu cin zarafi (Criminal Assault) na uku batanci (Defamation of Character), kuma da wahala ta tsallake wadannan laifuka da na zayyano

Hadiza Gabon da Amina Amal duk ba ‘yan Nigeria bane, sun fito daga kasashen renon Faransa, sun shigo mana Nigeria da tarbiyyansu irin na Faransa sunzo suna lalata mana tarbiyyan al’umma a Nigeria, ba zamu yarda da wannan iskancin ba

Allah Ya shiryeku, idan ba zaku shiryu ba Allah Ya mana maganinku

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button